Wednesday 2 March 2016

Girl In Abuja Cannot Locate Her Home & Parents(Pics)

Her name is Zulaihar Adam. She left Kaduna to serve as a nanny to a family based in Mararrabar, Abuja. She was sent on an errand by her employers but she can’t locate her way back. She does not also know the street  or address of the resident. That is all I can comprehend. If you know her or any member of her family kindly call 07069139120, 07056947154 or 08033634467. For those who read and understand Hausa fluently, kindly interpret. Read what Rariya posted on facebook below;

Bacewar 'Yar Shekara 12 Daga Garin Kaduna Zuwa Abuja

Daga Aliyu Ahmad

Wata yarinya 'yar shekara sha biyu mai suna Zulaihat Adam ta tsinci kanta cikin mawuyacin hali sakamakon kuntata mata da wata mata da aka kai ta aikin gida a wurinta daga garin Kaduna zuwa Mararrabar Abuja da jihar Nassarawa take yi.

A yayin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin yarinyar kan musabbabin bacewar tata, Zulaihat ta bayyana cewa "tun farko dama wadda nake yi wa aikin gidan tana kuntata min, amma babu yadda na iya saboda an kawo no ne wurinta da nufin na dinga yi mata aiki tana biya na a duk wata.

"Dalilin fitowar tawa daga gidan da naka aikin a yau shine, matar ta zarge ni da yin amfanin da sabulun wankarta, duk da cewa ban taba mata sabulun ba, ya fada cikin ruwa ne sai ni kuma na ciro na ajiye shi, amma sai ta yi zargin na yi amfani da shi, wanda sakamakon haka ne ta yi ta duka na, ni kuma sai na fito na gudu saboda azabar bugun da na sha."

Zulaihat ta kara da cewa kasancewar ba ta cika fitowa wajen ba a matsayinta bakuwa kuma 'yar aikin gida, hakan ya sa ta bata kuma ba ta san inda za ta je ba, wanda a dalilin kukan da take yi ne sai wasu mutane suka ajiye ta a wurinsu, inda ta zayyana musu duk abubuwan da suka faru da ita.

A yayin da aka tambayi Zulaihat ko daga wane yanki ta fito a Kaduna, ta bayyana cewa "mu 'yan asalin garin Gubuci ne, amma a Tudun Wada muke da zama, ta wajen bayan Masallacin Sheik Dahiru Bauchi. A kusa da Kasuwar Barci.

"Mahaifina mai suna Malam Adamu, wanda ake yi wa lakabi da Ya Hujja, kafin rasuwarsa yana sayar da shayi ne a garin Gubucci, daga baya kuma ni da mahaifiyata mai suna Rahina muka koma Kano da zama, kafin daga bisani kuma muka dawo wajen Masallacin Dahiru Bauchi dake Kaduna da zama. Ina da kannai masu suna Kabiru Bara'atu wadanda mahaifiyarmu daya da su, sai kuma 'yan kishiyar mamana mai suna Rabi, wadda 'yar asalin gaein Ikara ce, masu suna Yakubu da Bariyya.

Zulaihat ta ce an fi sanin gidansu da gidan Maman Nafisa.

Yanzu haka dai Zulaihat ba ta san inda za ta je ba, domin ta mance sunan unguwa da gidan da aka kawo ta aiki. Sannan kuma babu wanda ta sani, sai wadanda suka tsince ga a nan garin Mararraba dake iyakar Abuja da jihar Nassarawa.

Akwai bukatar a yada labarin don gan

Source: http://www.trezzyblog.com/2016/03/this-young-girl-based-in-abuja-cannot.html

No comments:

Post a Comment